Isa ga babban shafi

Birtaniya zata soma jigilar bakin haure zuwa kasar Rwanda - Kotu

Kotun Birtaniya a jiya juma’a ta amince da soma dawo da bakin aure zuwa kasar Rwanda, kamar  yada kasashen biyu Rwanda da Birtaniya suka cimma a wata yarjejeniya tsakanin su .

Tarin yan gudun hijira da hukumomin Birtaniya suka kama
Tarin yan gudun hijira da hukumomin Birtaniya suka kama AFP - GLYN KIRK
Talla

A cewar babban alkalin kotu na Landan ,Jonathan Swift,ya zama wajibi cikin  gaggawa a aiwatar da wannan doka da ta shafi  almarin baki yan Cin rani daga nan Birtaniya zuwa Rwanda.

Wasu rahotanni daga fadar Saurauniyar Ingila,Yarima Charles mai shekaru 73 a duniya ya bayyana takaicin sa tare da nuna adawa dangane da wannan mataki daga kotun Birtaniya.

Da jimawa a cewar wata jaridar kasar Birtaniya,an ji Yarima Charles bayyana dammuwa a kan wannan al'amari na bakin haure.

A kasar ta Rwanda za a gudanar da taron kasashen Commonwealth daga ranar 20 ga watan yuni, taron da ya dace Yarima Charles ya halara,yayinda wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil Adama suka soma sukar matakin na Birtaniya.

Sanarwar alkalin kotun ta hadu da fushin kungiyoyi dake kare hakokkin baki yan cin rani da suka hada Care 4 Calais da detention Action,wanda nan take suka  shigar da kara .

A Birtaniya,bangaren yan adawa sun nuna da wannan  yarjejeniya tsakanin Rwanda da kasar,yan adawa na zargin gwamnati da neman  kawo rudani a wani lokaci da farin jinin  Firaministan kasar Borris Johnson ke ragguwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.