Isa ga babban shafi

Bankin Duniya zai taimakawa Afrika da dala miliyan 315 don samar da abinci

Bankin Duniya ya ware dala miliyan 315 domin tallafawa wajen samun wadatar abinci a nahiyar Afrika, sai dai a wannan karon Najeriya ba ta cikin jerin kasashen da za su amfana da wannan tallafi. A farkon makon nan ne dai Bankin Duniyar ya fitar da tsarin jadawalin zango na biyu na shirin tallafawa kasashen na Afirka.

Matsalar yunwa na ci gaba da ta'azzara a kasashen Afrika, musamman yankin gabashi da ya shafe shekaru 5 yana fama da fari.
Matsalar yunwa na ci gaba da ta'azzara a kasashen Afrika, musamman yankin gabashi da ya shafe shekaru 5 yana fama da fari. AP
Talla

Karin mutane miliyan 2 daga kasashen Chadi, Ghana da kuma Saliyo ake sa ran za su amfana da tallafin na bankin duniya wanda zai taimaka wajen kara inganta noma da magance matsalolin karancin abinci da kuma rage kaifin tasirin sauyin yanayi.

Bankin Duniyar dai bai yi karin bayani kan dalilan da suka sa bai sanya Najeriya cikin kasashen da za su amfana da tallafin ba, wanda kuman ko a zangon farko ma haka abin ya ke, domin kasar ta rasa damar.

Amfana da dala miliyan 330 da Bankin ya fara warewa a cikin watan Nuwamban shekarar 2021, wanda aka kaddamar a watan Yunin shekarar 2022 da mu ke, tallafin da ya hada kasashen Burkina Faso, Mali, Jamhuriyar Niger, da Togo.

Kawo yanzu kimanin dalar amurka biliyan 18 bankin duniya ya bayar ga kasashe da dama a matsayin tallafi cikin shekaru uku da suka gabata, inda kuma kashi 54 cikin dari na adadin kudin ya tafi ga kasashen Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.