Isa ga babban shafi

Mayakan M23 sun fara janyewa daga yankunan da suka kwace a Congo

Rahotanni daga Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo na cewa mayakan ‘yan tawayen M23 sun fara janyewa daga yankunan da suka kwace iko da su a gabashin kasar, matakin da ke zuwa bayan jibge karin dakarun kasashen ketare a yankin. 

'Yan tawayen M23 ke barin wasu yankunan da suka mamaye.
'Yan tawayen M23 ke barin wasu yankunan da suka mamaye. REUTERS - JAMES AKENA
Talla

Majiyoyin Soji da na fararen hula sun tabbatarwa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP batun janyewar mayakan na M23 wadanda a baya suka kwace garuruwa da dama a lardin na arewacin Kivu da ke gabashin kasar bayan gwabza yaki na tsawon watanni tsakaninsu da dakarun gwamnatin Congo. 

Shugaban mayakan sa kai na garin Mweso da ke yankin Masisi mai tazarar kilomita 100 da birnin Goma fadar gwamnatin lardin na Kivu, Alphonse Habinna ya shaidawa AFP ta wayar tarho cewa basu da masaniya kan dalilin janyewar dakarun. 

Sai dai duk da wannan janyewa, Mayakan na M23 na kuma ci gaba da gwabza fada tsakaninsu da dakarun Congo wadanda ke samun taimakon sojojin kasashen gabashin Afrika 7 a yankuna da dama bayan lardin na Kivu. 

Duk da shiga tsakanin da Rwanda ta yi wanda ya kai ga kulla yarjejeniyar tsagaita wuta, bangarorin biyu sun koma kai wa juna farmaki kasa da mako guda bayan cimmajituwar a ranar 7 ga watan nan, inda a baya-bayan nan M23 ta yi barazanar katse hanyar da ta hada iyakokin Congo da Rwanda bayan karakarfin da sukayi a gab da birnin Goma. 

Wannan mataki na M23 na zuwa ne a daidai lokacin da jami’na diflomasiyya ke tsaka da tattaunawa a kokarin kawo karshen yankin na tsawon shekara guda da ya tagayyara tarin iyalai. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.