Isa ga babban shafi

Jamus ta kori jakadan Chadi a matsayin martani kan korar na ta

Gwamnatin Jamus ta kori jakadan Chadi, wanda ta bai wa wa’adin sa’o’i 48 da ya fice daga kasar. 

Shugaban rikon kwarayar gwamnatin sojin Chadi, Janar Mahamat Idris Deby Itno.
Shugaban rikon kwarayar gwamnatin sojin Chadi, Janar Mahamat Idris Deby Itno. © presidence du Chad
Talla

Matakin na Jamus dai na a matsayin martani ga korar na ta jakadan da Chadi ta yi a makon da ya gabata. 

Korar Jakadan Jamus Gordon Kricke daga Chadi ya biyo bayan sukar gwamnatin sojin kasar da ya yi akan jinkirta gudanar da zaben sake mikawa farar hula mulki, da kuma hukuncin kotun da ya baiwa shugaban soji mai ci Mahamat Idris Deby damar sake neman shugabancin kasar cikin rigar siyasa. 

Jim kadan bayan kalaman ne gwamnatin Chadi ta bayyana su a matsayin raini gare ta, lamarin da ta ce baza ta lamunta ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.