Isa ga babban shafi

An fara shirin jana'izar mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a Rwanda

Mutanen Kasar Rwanda na ci gaba da juyayin mutuwar ‘yan uwan su da kuma gidajensu da suka rushe sakamakon ambaliya da kuma zabtarewar kasar da aka samu wanda ya hallaka mutane akalla 130 da kuma rushewar dubban gidaje. 

Yadda mutane ke fama bayan da ambaliya ta aukawa. kasar Rwanda
Yadda mutane ke fama bayan da ambaliya ta aukawa. kasar Rwanda AP
Talla

Yayin da gwamnati ke ci gaba da tattara alkaluman irin asarar da aka tafka, ‘yan uwan wadanda suka mutu na shirin gudanar da jana’iza, yayin da wadanda suka rasa matsugunan su ke neman mafaka. 

Hukumar agajin gaggawa a kasar tace gidajen da suka rushe sun zarce 5,100, yayin da wasu sama da 2,500 suka lalace. 

Ana saran Firaministan kasar Eduard Ngirente ya ziyarci yankunan da aka samu iftila’in yau alhamis. 

Ana saran gwamnati ta tallafawa akalla iyalan mutane 100,000 da suka rasa ‘yan uwan su da Dala 110 kowannen su. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.