Isa ga babban shafi

Kasashen duniya suna sane suka yi biris da rikicin Burkina Faso - Norway

Kungiyar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta kasar Norway ta koka game da yadda duniya ta yi watsi da tashin hankalin da ke faruwa a Burkina Faso, kawai saboda siyasa ko kuma biyan bukatar wata kasa. 

Kasar dai na fama da rikicin masu tayar da kayar bayan tun shekarar 2015.
Kasar dai na fama da rikicin masu tayar da kayar bayan tun shekarar 2015. © RFI
Talla

Ta cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, mai dauke da sa hannun shugaban ta Jan Egeland ya ce wannan biris da duniya ta yi da halin da kasar ke ciki ya jefa rayukan miliyoyin mutane cikin hadari. 

A  cewar sanarwar abin takaici ne yadda kasashe masu fada aji ke watsi da lamuran kasashen African da suka nuna turjiya ga wasu bukatun su, tare da fifita wadanda suka zama karen farautar su, wanda kuma hakan na karewa ne kan fararen hula da basu ji ba basu gani ba. 

Burina Faso, wadda sojoji suka kwace ragamar mulkinta a shekarar 2022 tana fama da matsalar ‘yan ta’addda masu ikirarin jihadi da ke shiga kasar daga Mali tun daga shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.