Isa ga babban shafi

Gambia ta kammala bincike kan maganin tarin India da ya kashe yara 70

Sakamakon binciken da mahukuntan Gambia suka fitar ya tabbatar da cewa nau’ikan magunguna tarin nan 4 da aka shigar da su kasar daga India ne suka sabbaba mutuwar kananan yara 70 a shekarar da ta gabata.

Wasu Iyaye da ke bore kan yadda maganin tarin ya kashe musu 'ya'ya.
Wasu Iyaye da ke bore kan yadda maganin tarin ya kashe musu 'ya'ya. © REUTERS - EDWARD MCALLISTER
Talla

Ministan lafiyar Gambia Dr Ahmadou Lamin Sametah ya bayyanawa taron manema labarai cewa wadanda suka shigar da maganin basu cika matakan shigar da kayaki kasar ba, hasalima nau’ikan maganin basu samu sahalewar hukumar kula da magunguna ta yammacin Afrika ba.

Rahotannin sun bayyana yadda yaran 70 suka kamu da cutar koda gabanin mutuwa bayan amfani da nau’ikan maganin na India.

Ministan ya ce tuni aka tube ilahirin jami’an hukumar kula da magunguna na kasar haka zalika tawagar jami’an da suka sanya idanu kan magungunan da ke shigowa daga ketare saboda samunsu da sakaci wajen gaza tantance maganin har ya kai ga kisan yara 70.

Akalla yara 300 maganin tarin samfurin India ya kashe a kasashen Gambia da Uzbekistan da kuma Indonesia a shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.