Isa ga babban shafi

Morocco ta roki Algeria ta bude iyakokinta don dawowar hulda tsakaninsu

Sarki Mohammed na 5 ya bayyana cewa fata guda da Morocco ke da shi shi ne dawowar kyakkyawar hulda tsakaninta da makwabciyarta Algeria tare da budewa juna iyakokin duk da tabarbarewar huldar diflomasiyyar da ke tsakaninsu.

Sarkin Morocco Mohammed na biyar.
Sarkin Morocco Mohammed na biyar. © Moroccan Royal Palace / AFP
Talla

Tun bayan rikicin kasashen biyu mafiya karfin fada aji a yankin Maghreb cikin shekarar 1994, har yanzu iyakokinsu na ci gaba da kasancewa a kulle duk kuwa da yadda Morocco ke ci gaba da bukatar budesu a lokuta daban-daban.

A shekarar 2021 ne Algeria ta sanar da katse dukkanin wata hulda tsakaninta da Morocco baya ga dakatar da aikin ginin bututun gas dinta da zai ratsa kasar zuwa Spain haka zalika ta haramtawa jiragen makwabciyarta ta damar sauka ko keta sararin samaniyarta.

Cikin fiye da shekaru 2 dai tsakanin kasashen biyu babu wadda ta ke da wakilcin jami'an diflomasiyya a makwabciyar ta ta, bayan da tun farko Algeria ta janye jakadunta biyo bayan takun saka.

Sai dai duk da haka Sarki Mohammed ya bayyana fatar wata-rana a kusa ko a nesa alakar kasashen biyu ta dawo kamar yadda ta ke kafin rikicin shekarar 1994 don ci gaba da kasancewa 'yan uwan juna.

A cewar sarki Mohammed bukatar su a yanzu shi ne Algeria ta amince da bude iyakokinta ga Morocco don saukakawa al'ummominsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.