Isa ga babban shafi

Faransa ta karyata neman hadin kan Algeria don amfani da karfin soja kan Nijar

Rundunar sojin Faransa ta karyata rahotannin da ke cewa ta nemi gwamnatin Algeria ta ba ta damar yin amfani da sararin samaniyar kasar wajen amfani da karfin soja kan Jamhuriyar Nijar.

Daya daga cikin jiragen yakin rundunar sojin kasar Faransa kirar Rafale.
Daya daga cikin jiragen yakin rundunar sojin kasar Faransa kirar Rafale. AP - Francois Mori
Talla

Faransa ta fitar da sanarwar ce bayan da wani gidan rediyo a Algerian da ya saba sanar da matakai da sauran manufofin gwamnatin kasar, ya bayar da rahoton cewar mahukuntan sun ki amincewa da bukatar Faransawan.

A farkon watan nan na Agusta, shugaban Algeria AbdelMajid Tebbounne ya bayyana fargaba kan abinda ka iya biyo bayan amfani da karfin soja a Nijar, matakin da ya ce zai iya haddasa tabarbarewar tsaro a baki  dayan yankin Sahel, dan haka kasarsa ba za ta yi  amfani da karfi akan makotanta ba.

Sojoji kimanin dubu 1,500 Faransa ta girke a Nijar kafin juyin mulkin da sojoji suka yi a watan da ya gabata, har yanzu kuma Faransar ba ta ce za ta yi  amfani da karfin soja wajen maido da mulkin farar hula a kasar ba.

A makon da ya gabata, kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS ko CEDEAO ta bayyana cewar ta tsayar da ranar daukar matakin soji kan sojojin Nijar da suka yi juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli idan bukatar hakan ta taso, muddin matakkan diflomasiya suka gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.