Isa ga babban shafi

Algeria ta tura wakili don tattaunawa d sojojin Nijar

Gwamnatin Algeria ta ce ta aike da Sakatare Janar na Ma’aikatar Harkokin Wajenta, Lounes Magramane zuwa Nijar a wannan Alhamis a wani bangare na inganta alakar diflomasiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a makwabciyar kasar.

Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune  kenan.
Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune kenan. © reuters
Talla

Hakan dai na zuwa ne kwana guda bayan Ministan Harkokin Wajen Algeria, Ahmed Attaf ya fara rangadi a kasashen yammacin Afirka da nufin lalubo bakin zaren warware rikicin siyasar Nijar, inda gwamnatin Algiers ke adawa da duk wani tsoma bakin soji bayan juyin mulkin.

Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS ta yi barazanar amfani da karfi wajen mayar da zababben shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum kan kujerarsa, wanda sojoji suka tsare a ranar 26 ga watan Yuli.

Algeria wadda ke da iyaka da Nijar mai nisan kilomita 1,000 a kudancin kasar, ta yi gargadin daukar matakin soji, inda shugaba Abdelmadjid Tebboune ya ce zai zama barazana kai tsaye ga kasarsa.

Kasar na da iyaka da Libya da Mali, wadanda suka kasance a cikin tashe-tashen hankali na tsawon shekaru.

Nijar ita ce kasa ta hudu a yammacin Afirka tun shekarar 2020 da aka yi wa juyin mulki, bayan Burkina Faso da Guinea da kuma Mali.

Hukumomin mulkin sojan Burkina Faso da Mali sun ce duk wani tsoma bakin soji a makwabciyarsu za su dauke shi a matsayin shelanta yaki a kan kasashensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.