Isa ga babban shafi

Hambararren shugaban Gabon ya roki a ceto shi daga daurin talalar da aka masa

Shugaba Ali Bongo na Gabon, wanda sojojin da ke tsaron fadarsa suka yi masa juyin mulki ya yi roko a taimaka a ceto shi daga daurin talalar da aka yi masa.

Hoton bidiyon da Ali Bongo ya yi a wani wuri da  ba a fayyace ba. 8 Agusta, 2023.
Hoton bidiyon da Ali Bongo ya yi a wani wuri da ba a fayyace ba. 8 Agusta, 2023. AFP - -
Talla

A wani faifen bidiyo da aka wallafa a shafukan sadarwar zamani dabam-dabam, an jiyo hambararren shugaban yana bukatar  wadanda ya  kira 'abokansa a fadin duniya’ su fito su nuna rashin amincewarsu da abin da ya faru.

Sojojin da suka kifar da gwamnatin Gabon su kuma yi wa shugaba Bongo da wasu daga cikin iyalansa daurin talala a cikin fadar gwamnatin kasar.

Da asubahin wannan rana ta Laraba ce masu juyin mulkin Gabon din suka hambarar da gwamnati, suka kuma sanar da soke sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, wanda aka ayyana Bongo a matsayin wanda ya yi nasara.

Sojojin sun kuma sanar da rushe dukkannin hukumomi na kasar, majalisar dokoki tare da rufe kan iyakoki, suna mai cewa suna aiki ne da yawun rundunar tsaron kasar.

Wannan ne karon farko da aka ji daga hambararren shugaban na Gabon tun bayan juyin mulkin da aka masa da sanyin safiyar Larabar nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.