Isa ga babban shafi

Gabon: Sojoji sun bai wa Ali Bongo damar fita waje neman magani

Sojoji da suka yi juyin mulki a Gabon, sun bai wa hambarerren shugaban kasar Ali Bongo da ke tsare damar  yin balaguro zuwa kasashen waje domin duba lafiyarsa.

Hambarerren shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba, yayin haklartan taron AU. 18/02/23
Hambarerren shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba, yayin haklartan taron AU. 18/02/23 AFP - EDUARDO SOTERAS
Talla

Jagoran juyin mulkin Janar Brice Oligui Nguema wanda ya hambarar da Ali Bongo ya kuma sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban rikon kwarya ya ce mista Bongo na da cikakken ‘yanci, kamara yadda ya bayyana cikin sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar.

"Yana da 'yancin walwala... ciki harda tafiya kasashen waje idan ya ga dama," in ji Janar Brice Oligui Nguema

Bongo, wanda ya shafe shekaru 14 a kan karagar mulki, ya kasance a tsare tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 30 ga watan Agusta, kasa da sa'a guda bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da nasara sa ta yin tazarce, wanda jam’iyyun adawa suka bayyana a matsayin an tafka magudi.

"Idan aka yi la'akari da yanayin lafiyarsa, tsohon shugaban kasar Ali Bongo Ondimba yana da 'yancin yin tafiya, zai iya tafiya kasashen waje idan yana bukatar duba lafiyarsa," in ji Kanar Ulrich Manfoumbi Manfoumbi, yayin karanta wata sanarwa da Oligui ya sanya wa hannu.

Rashin lafiyar Bongo

Bongo na fama da matsananciyar ciwo na shanyewar jiki tun a watan Oktoban 2018 wanda hakan ya sa ya samu nakasu a jiki, wanda ya haifar masa da cikas musamman wajen motsa kafarsa da hannunsa ta dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.