Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Gabon ta kaddamar da majalisar zartaswa

Shugaban gwamnatin sojin Gabon Janar Brice Oligui Nguema ya kaddamar da majalisar zartaswar gwamnatin sa, ciki kuwa har da ‘yan siyasa daga jam’iyyun kasar daban-daban.

Ana dai ganin wannan tsari da sojojin suka zo da shi na shigar da kowanne bangare cikin gwamnati zai taimaka kwarai wajen hadin kan kasar
Ana dai ganin wannan tsari da sojojin suka zo da shi na shigar da kowanne bangare cikin gwamnati zai taimaka kwarai wajen hadin kan kasar AFP - -
Talla

Kunshin majalisar zartaswar ya hadar da tsaffin masu baiwa hambararren shugaban kasar shawara, da tsaffin ministoci, jami’an soji da kuma ‘yan kungiyoyin fararen hula.

Sai dai bayanai sun ce majalisar zartaswar bata kunshi fitattun mutane a gwamnatin Ali Bongo Odimba ba.

Mr. Ndong Sima shine aka nada a matsayin wanda zai jagoranci kafa gwamnatin rikon kwarya, bayan juyin mulkin da ya yi tafiyar ruwa da Ali Bongo Odimba, jim kadan bayan sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Duk da dai babu wani kayaddaden lokaci da sojoji suka fitar na mayar da gwamnati hannun farar hula, sai dai ana ganin tamkar basu kwaci gwamnati don tabbata a kan mulki ba, kamar yadda suma suka sanar.

Kafa majalisar zartaswar mai kunshe da mutane 26 na zuwa ne kwanaki biyu bayan nada Ndong Sima mai shekaru 68 da ya rike mukamin Prime ministan kasar karashin gwamnatin shugaba Bongo, daga shekarar 2012 zuwa 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.