Isa ga babban shafi

Amurka da Norway za su taimakawa kananan manoman Afirka da dala miliyan 70

Kasashen Amurka da Norway sun kaddamar da wani shirin taimakawa kananan manoma a Afirka bunkasa ayyukansu da tallafin kudadden da suka kai Dala miliyan 70, da zummar ganin an dakile matsalar karancin abincin da ake fuskanta a sassan nahiyar.

Wani makekiyar gona a lardin Thies da ke kasar Senegal. 24 Janairu, 2023.
Wani makekiyar gona a lardin Thies da ke kasar Senegal. 24 Janairu, 2023. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Shugabar hukumar ci gaba ta Amurka, Samantha Power da takwararta ta Norway, Beathe Tvinnereim suka sanar da wannan sabon shirin a birnin New York, inda shugabannin kasashen duniya ke gudanar da taronsu na shekara shekara.

Masana na kallon wannan shiri a matsayin wani ci gaba na bangaren alaka tsakanin Amurka da Turai a bangare guda, da kuma Afirka a bangare guda, a daidai lokacin da a daya  bangaren China da Rasha ke kokarin janye kasashen Afirkan daga wurinsu.

Shi dai wannan tallafin na Dala miliyan 70 wanda Amurka da Norway za su zuba Dala miliyan 35 kowacce daga cikinsu, ana fatan ganin ya habaka zuwa Dala miliyan 200 nan gaba, saboda fatan gudumawar da ake sa ran samu daga masu bayar da agaji, yayin da ake son akalla mutane miliyan 7 da rabi a nahiyar Afirka su ci gajiyarsa.

Bayanan da kasashen biyu suka gabatar ya nuna cewa, tallafin na iya shafar kananan manoma da kuma ‘yan kasuwa 500, tare da manoma miliyan guda da rabi da kuma sana’o’i masu zaman kansu akalla dubu 60.

Ana fatan wannan asusun ya zaburar da miliyoyin daloli wajen kasuwanci ba tare da wata barazana da ake fuskanta wajen zuba jari ba.

A wannan shekarar an samu ruwan sama sosai sabanin hasashen da aka yi na samun fari a wasu yankuna, amma hakan bai hana kungiyoyin agaji bayyana cewar mutane kusan miliyan 60 ne ke fuskantar barazanar yunwa a kasashe 7 da ke gabashin Afirka.

Bayanai sun ce wasu miliyoyin jama’a a yankin Afirka ta yamma sun fuskanci karancin abincin sakamakon annobar Korona da Sauyin Yanayi da kuma hauhawan farashin kayayyaki.

Power ta ce rashin irin wannan tallafi ga kananan manoma ya kan shafi aikin noman ta hanyar yadda mutane kan iya noma abinda za su ci ne kawai.

Jami’ar ta ce da zarar an taimakawa kananan manoman da ingantaccen iri da kuma takin zamani, tare da inda za su sayar da amfanin gonakinsu ko kuma sarrafa su zuwa abinda jama’a za su yi amfani da shi, nan da nan za su samu habaka da kuma yaki da yunwa tare da talauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.