Morocco ta ware kusan dala biliyan 12 don sake gina yankunan da aka yi girgizar kasa
Gwamnatin Morocco ta sanar da ware dirham biliyan 120, kwatankwacin sama da dala biliyan 11 don sake gina yankunan da aka yi mummunar girgizar kasar.
Wallafawa ranar:
A wata sanarwa, gwamnatin ta ce ta ware kudaden ne don gudanar da aikin taimaka wa mutane miliyan 4 da dubu dari 2 da wannan girgizar kasa ta shafa a cikin shekaru 5 masu zuwa.
A ranar 8 ga watan Satumba ce girgizar kasa mai karfin maki 6 da digo 8 ta afkawa lardin Al-Haouz da ke kudancin Marrakesh, inda ta yi sanadin mutuwar mutane kusan dubu 3 tare da jikkata dubbai.
Girgizar kasar ta lalata dubban gidaje a yankin tsakiyar Morocco, ciki, abin da ya tilasta wa iyalai da dama kwana a waje cikin sanyi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu