Isa ga babban shafi
SAUYIN YANAYI

Oxfam ta sake bayyana damuwa a kan yadda manyan kasashe ke gurbata muhalli

Afirka – Kungiyar Agaji ta Oxfam ta sake bayyana matukar damuwa a kan yadda manyan kamfanonin kasashen duniya suka sake kara yawan sinadarin da suke fitarwa wadanda ke gurbata muhalli, wanda kungiyar tace ya karu da kashi 16 daga shekarar 2019 zuwa yanzu.

Alamar Oxfam
Alamar Oxfam REUTERS/Andres Martinez Casares
Talla

Wani rahoton da kungiyar ta fitar yau, ya bayyana cewar, wadannan sinadaren da kasashen da suka ci gaba ke fitarwa, na iya illa ga sama da rabin yawan abincin da kasashen Afirka ke nomawa da ya kunshi shinkafa da alkama da kuma waken soya.

Daraktan kungiyar dake kula da nahiyar Afirka, Fati N’zi Hassane tace manyan kasashen duniya dake da arzikin masana’antu na zama babban barazana ga rayuwar bil Adama a wannan duniyar.

Hassane tace abin takaici ne yadda jama’ar da ke ‘dan’dana azabar wannan matsala, musamman ‘yan Afirka basa taka rawa wajen haifar da ita, yayin da kuma basa shirya tinkarar matsalar wadda kungiyar mutane ‘yan kalilan ke samar da ita.

Masu zanga zangar adawa da gurbata muhallin dake neman ganin an lafta haraji a kan attajirai
Masu zanga zangar adawa da gurbata muhallin dake neman ganin an lafta haraji a kan attajirai © Oxfam

Kungiyar Oxfam tace ta samu rahoto na zahiri a kan yadda mutanen dake fama da talauci da suka hada da mata da ‘yam mata da mazauna yankunan karkara, ke shan azabar wannan matsalar ta sauyin yanayi, abinda ke dada haifar da gibi tsakanin masu arziki da matalauta.

Rahotan binciken da akayi ya bayyana cewar yawan mutanen dake mutuwa sakamakon ambaliya a kasashe matalauta ya zarce wadanda ake gani a kasashe masu arziki, abinda ke da’da nuna gibin dake tsakanin bangarorin biyu.

Oxfam tace gwamnatoci na iya shawo kan wannan matsalar na rashin daidaito a tsakanin jama’a da kuma sauyin yanayin wajen tinkarar yadda manyan kasashe masu arzikin masana’antu ke gurbata muhalli da kuma zuba jari a hanyoyin jin dadin jama’a.

Kungiyar tayi hasashen cewar kashi 60 na harajin wadannan manyan kasashe na iya dakile gurbata muhallin da ake samu a Birtaniya ta hanyar tara kudin da ya kai kusan dala triliyan 6 da rabi kowacce shekara, wajen amfani da su ta hanyar samar da makamashin da baya gurbata muhalli.

Yadda sauyin yanayi ke illa ga bangaren noma
Yadda sauyin yanayi ke illa ga bangaren noma © Irina Fuhrmann / AFP

Oxfam ta bukaci karkata akasarin wadannan kudade zuwa kasashe matalauta domin sauya hanyoyin samar da makamashi da taimakawa al’ummomi kare kansu daga radadin sauyin yanayin, da kuma biyan diyya ga wadanda suka tafka asara sakamakon matsalar.

Babban Daraktan kungiyar Oxfam na duniya, Amitabh Behar yace sun kwashe shekaru suna yaki da matsalar amfani da man fetur dake gurbata muhalli domin ceto rayukan miliyoyin jama’a da kuma duniyar da muke rayuwa.

Behar yace ya zama wajibi a bayyana karara cewar, rashin sanya haraji a kan dukiyar attajirai na iya basu damar yiwa jama’a illa wajen lalata musu matsugunai da kuma yiwa dimokiradiyarsu zagon kasa.

Jami’in yace lafta musu haraji zai taimaka gaya wajen magance matsalar rashin daidaito da kuma na sauyin yanayi, tare da karbo triliyoyin dalolin da za’a yi amfani da su wajen zuba jari a karni na 21 da zai inganta muhalli da bunkasa dimokiradiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.