Isa ga babban shafi

Yadda aka yi jana'izar jagoran adawar Kamaru duk da yana raye

‘Yan adawa a kasar Kamaru sun yi Allah wadai da wani dabi’a da wasu sarakun gargaji suka nuna a Yaunde babban birnin kasar na cin zarafin madugun ‘yan adawa Maurice Kamto na jam’iyyar MRC.

Yadda aka yi jana'izan hoton jagoran adawar Kamaru Maurice Kamto alhali yana raye. 26/11/23
Yadda aka yi jana'izan hoton jagoran adawar Kamaru Maurice Kamto alhali yana raye. 26/11/23 © N'ZUI MANTO
Talla

 

Hotunan bidiyo da ke yawo a kakafen sada zumunta sun nuna yadda sarakunan al’ummar Lekie ke dauke da akwatin gawa da aka likawa hotun Kamto, suna jana’izan mutumin da ke raye.

Kamto da ya fito daga bangaren kabilan Bamileke a Yammacin kasar shi ya zo  biyu a zaben shugaban kasar da ya gabata, inda Paul Biya mai shekaru kusan 90 da kabilun Eton da Beti ke marawa baya ya samu nasara.

Yadda aka yi jana'izan jigoran adawar Kamaru Maurice Kamto na jam'iyyar MRC alhali yana raye. 26/11/23
Yadda aka yi jana'izan jigoran adawar Kamaru Maurice Kamto na jam'iyyar MRC alhali yana raye. 26/11/23 © N'ZUI MANTO

Tun bayan takarar Maurice Kamto wanda babban lauya ne da ya sha taimakawa kasar a kotun kasa da kasa ciki harda shara'ar da aka mikawa Kamaru Bakasi, an samu rarrubuwa kawuna da cece kuce mai alaka da kabilanci.

MRC zata shirgar da kara

Tuni jam'iyyar MRC ta sanar da shirin daukar matakin shari'a kan shugabannin na al'ummar Lekie dangane da abin da sakataren jam'iyyar Emmanuel Ateba ya kira ba'abin lamunta ba ne.

Wannan lamari dai ya haifar da muhara mai zafi tsakanin 'yan kasar da ma kafafen radiyo da talabijin, wasu na danganta lamarin da shagube, yayin da wasu ke cewa tsafe-tsafe ne na karya logon farin jinin jigon na adawa Maurice Kamto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.