Isa ga babban shafi

Kotu a Jamus ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga wani dan kasar Gambia

A yau Alhamis a kasar Jamus,wani alkalin kotu ya zartas da hukunci na daurin rai-da rai ga wani dan kasar Gambia, bisa samunsa da laifin shiga cikin kungiyar nan da ta aikata kisan gilla a karkashin gwamnatin shugaba Yahya Jammeh na Gambia.

Bai Lowe daya daga cikin masu aiki da kungiyar  masu kisa ta Junglers a Gambia
Bai Lowe daya daga cikin masu aiki da kungiyar masu kisa ta Junglers a Gambia AFP - RONNY HARTMANN
Talla

Daga cikin tuhume-tuhume da ake yiwa Bai Lowe harda da kisan gillar da aka yi wa wani dan jarida na AFP a lokacin.

Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh.
Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh. AP - Jerome Delay

Kotun da ke garin Celle da ke arewacin Jamus ta samu Bai Lowe da laifukan cin zarafin bil adama, kisa da kuma yunƙurin kisan kai a matsayinsa na direban wannan kungiya, ƙungiyar 'yan sa-kai da gwamnati ta samar a lokacin shughabancin Yahya Jammeh wanda aka haifa a ranar 25 ga watan Mayu na shekarar 1965.

Kungiyoyi da dama ne suka shigar da kara don ganiun an kama tsohon Shugaban kasar ta Gambia.

tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh yayin gaisawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Banjul. 13/12/2016.
tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh yayin gaisawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Banjul. 13/12/2016. REUTERS/Stringer

Jammeh da iyalansa sun tafi gudun hijirar siyasa, wanda ya kawo karshen mulkin tsoro na shekaru 22 da kuma takun sakar siyasa bayan zaben da ya yi barazanar haifar da tsoma bakin sojojin yankin a lokacin da ya makale kan karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.