Isa ga babban shafi
SAHARAWI

MDD ta bukaci Morocco ta saki gomman fursunonin da take tsare da su

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Morocco da saki gomman fursunonin da ke tsare a hannunta cikin masu fafutukar ‘yancin yankin yamma da sahara ko kuma Sahrawi na kungiyar Gdeim Izik da aka kame tun a shekarar 2010 yayin wani gangami da kungiyar ta jagoranta.

Wata mace dake shela a wurin zanga-zangar neman 'yancin yankin Saharawi a birnin Madrid ranar 16 ga uwamba, 2014.
Wata mace dake shela a wurin zanga-zangar neman 'yancin yankin Saharawi a birnin Madrid ranar 16 ga uwamba, 2014. AFP PHOTO/ JAVIER SORIANO
Talla

Cikin gomman shekaru da suka gabata, Moroccon ta kame tarin masu fafutukar ‘yancin yankin na Sahrawi da bayanai ke cewa yawansu ya kai 25, sai dai sanarwar Majalisar ta yau Litinin, ta bukaci lallai gwamnatin kasar ta saki mutanen cikinsu har da ‘yan jarida da masu kare hakkin dan adam.

Tun a shekarar 1975 Morocco ta kwace iko da yankin na Yammacin Sahara Wanda girmansa ya yi kwatankwacin 2 bisa 3 na fadin kasar, duk da cewa har zuwa yanzu Majalisar Dinkin Duniya ba ta amince da kasancewar yanki wani bangare na kasar ba.

Daftarin da Majalisar Dinkin Duniya ta kammala tattarawa a watan Oktoba, ya bukaci gwamnatin Morocco da ta yi gaggawar sakin wadanda take tsare da su.

Daga cikin wadanda ke tsaren akwai 'yan jarida, da kuma masu fafutukar kare hakkin dan adam.

Rahoton ya ci gaba da cewa, an cafke mutanen ne tun a shekarar 2010, lokacin da suka shiga zanga-zangar da ta gudana a yankin Gdeim Izik da aka mamaye, wadanda ke neman a bawa al'ummar yankin na Saharawi 'yancin cin gashin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.