Isa ga babban shafi

Wata fashewa bayan hadarin tankar dakon gas ta kashe mutane 40 a Liberia

Ana fargabar mutuwar mutane fiye da 40 a wata gobara da ta tashi bayan fashewar wata tankar dakon gas a arewacin Liberia.

Ana alakanta yawaitar hadarin mota kan rashin kyawun tituna ko kuma gudun wuce sa'a.
Ana alakanta yawaitar hadarin mota kan rashin kyawun tituna ko kuma gudun wuce sa'a. SANA/AFP
Talla

Babban jami’in lafiyar yankin Totota da ibtila’in ya faru Francis Kateh ya tabbatarwa manema labarai a jiya Laraba cewa akwai gawarwakin akalla mutane 40 baya ga wasu da dama da suka jikkata kuma suke karbar kulawar gaggawa yanzu haka a asibiti.

Rahotanni sun ce a daren Talatar da ta gabata ne, tankar dakon gas din ta yi hadari a yankin na Totota da ke lardin Bong kuma nan take ta fashe lamarin da ya hallaka tarin mutanen da ke gab da ita.

Francis Kateh ya shaidawa manema labarai cewa adadin ka iya karuwa lura da gomman mutanen da ke asibiti galibinsu a mawuyacin halin.

Ana dai alakanta hadarin motar da ake yawan samu a Liberia kan lalacewar hanyoyi dalilin da ya mayar da kasar ta yammacin Afrika mafi yawan fuskantar hadarin mota tsakanin takwarorinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.