Isa ga babban shafi

Gwamnatin Saliyo ta fara tuhumar tsohon shugaban kasar kan cin amana

Gwamnatin Saliyo ta fara tuhumar tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma da laifin cin amanar kasa a sakamakon zargin sa da hannu a yunkurin juyin mulkin watan Nuwamban bara.

Ernest Bai Koroma,
Ernest Bai Koroma, © Michèle Spatari / AFP
Talla

Da yake karanto tuhumar a gaban kotun, babban mai gabatar da kara na kasar ya ce wadanda aka samu da hannu dumu-dumu a yunkurin juyin mulkin na cikin manyan dogaran tsohon shugaban kasar da kuma mambobin kwamitin koli kan harkokin tsaro a gwamnatinsa.

Bayanai sun ce, magoya bayansa sun fashe da kuka bayan da aka sanya sunanansa cikin jerin wadanda ake tuhuma da laifin cin amanar kasar.

Ranar 26 ga watan Nuwamban bara ne dai aka wayi gari da hari kan barikokin sojoji da gidajen yari, abin da ya bai wa daurarru sama da dubu 2,200 damar tserewa yayin da fiye da 20 suka mutu, abin da mahukunta suka kwatanta da yunkurin kifar da gwamnati mai ci.

Tuni aka gurfanar da mutanen a gaban kotun Majistrate da ke babban birnin kasar wato Freetown kamar yadda Ma’aikatar Yada Labarai ta kasar ta bayyana. 

Tun bayan yunkurin juyin mulkin gwamnatin ta alakanta shi da magoya bayan tsohon shugaba Koroma musamman masu tsaron lafiyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.