Isa ga babban shafi

Cape Verde ta kawo karshen zazzabin cizon sauro

Cape Verde ta zama kasa ta uku a Nahiyar Afrika da ta kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro, duk kuwa da dubban mutanen da cutar ta yi ajalin su a kasar.

Sauro mai haddasa cutar malaria
Sauro mai haddasa cutar malaria © Shutterstock/mycteria
Talla

Kasar mai yawan mutane kusan dubu 600 ta biyo bayan kasashen Mauritius da kuma Algeria da suma suka kawo karshen cutar.

A shekarar 2021 Kasar ke da kaso mafi yawa daga kaso 95 na alummar nahiyar Afirka da ke kamuwa da zazzbin cizon sauro, kuma ke da kaso mafi yawa daga kashi 96 na mutanen da suka mutu a wannan shekara.

Kasashe 43 ne dai suka yi nasarar fatattakar cutar a fadin duniya abinda ke nuna sannu a hankali kasashe na nasarar mayar da cutar da ke saurin hallaka dan adam tarihi.

Director-General of the World Health Organisation (WHO) Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus attends an ACANU briefing in Geneva, Switzerland, December 15, 2023.
Darekta janar na Hukumar lafiya ta duniya Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus REUTERS - DENIS BALIBOUSE

Da yake jawabi shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce tabbas Cape Verde ta yi abin a yaba, kuma akwai bukatar sauran kasashen Afrika su yi koyi da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.