Isa ga babban shafi

Algeria ta ji takaici kan matakin Mali na soke yarjejeniyar sulhu da 'yan tawaye

Algeria ta bayyana takaicinta bayan da gwamnatin sojin Mali da ke makwabtaka da ita ta soke soke yarjejeniyar zaman lafiya da ta shiga tsakani aka kula tsakanin gwamnatin kasar ta yammmacin Afirka da ‘yan aware a shekarar 2015.

Shugaban Algeria,  Abdelmadjid Tebboune.
Shugaban Algeria, Abdelmadjid Tebboune. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Kungiyoyi masu ikararin jihadi da ‘yan aware a Mali sun fara tada kayar baya a kasar tun a shekarar 2012, kuma Algeria ce ta shiga Tsakani har aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnati da kungiyar ‘yan awaren Abzinawa.

 

Amma a ranar Alhamis da ta gabata gwamnatin sojin Mali ta sanar da kawo karshen wannan yarjejeniya, biyo baya watannni da aka shafe ana gwabza fada sakamakon umurin barin kasar da gwamnati ta bai wa rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkiin Duniya.

Gwamnatin sojin Mali, wadda ta ce ta zo ne don warware matsalar tsaro da ta addabi kasar tana daukar matakai dabam-dabam don ganin ta cimma wannan buri nata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.