Isa ga babban shafi

Kotun ta bayyana haramcin tura 'yan sanda dubu zuwa kasar Haiti daga Kenya

Wata kotu  a Kenya ta soke matakin da gwamnatin kasar ta dauka na tura jami'an 'yan sanda dubu zuwa kasar Haiti, wanda ya sabawa tsarin mulki, tsarin na daga cikin shirin  tawagar da Majalisar Dinkin Duniya na marawa don kokarin kawo karshen tashe-tashen hankulan 'yan daba a Haiti.

Yan Sandan kasar Kenya a Haiti
Yan Sandan kasar Kenya a Haiti AP - Odelyn Joseph
Talla

 

Hukuncin da babbar kotun birnin Nairobi ta yanke ya nuna dakatar da dakarun kasa da kasa da ake sa ran za su yi kokarin kwantar da tarzoma a kasar ta Haiti dake kusan karamar jiha a tsibirin Caribbean, inda tashe-tashen hankula suka yi sanadiyar mutuwar kusan mutane 5,000, ciki har da fararen hula fiye da 2,700  a shekarar 2023.

Wasu daga cikin yan sandan kasar Kenya a Haiti
Wasu daga cikin yan sandan kasar Kenya a Haiti © Tony Karumba / AFP

Yayin da ake ci gaba da fuskantar kiraye-kirayen daga gwamnatin Haiti da Majalisar Dinkin Duniya, Kenya ta amince a watan Yulin 2023 don jagorantar wannan runduna ta 2,500 zuwa 2,600 zuwa kasar ta Haiti kamar dai yada aka cimma yarjejeniya tsakanin kasar ta Haiti,Kenya da Majalisar dimkin Duniya,tsarin da ke samun goyon bayan Amurka.

Wani dan sandan Kenya yayi tarzoma  a Haiti
Wani dan sandan Kenya yayi tarzoma a Haiti © Luis Tato / AFP

Sai dai sanarwar da gwamnatin Kenya ta fitar, wadda ta tabbata a majalisar dokokin kasar a ranar 16 ga watan Nuwamba, ta haifar da gagarumar zanga-zanga a wannan kasa ta gabashin Afirka.

 

Wani dan adawa Ekuru Aukot dai ya daukaka kara zuwa babbar kotun birnin Nairobi, yana mai cewa wannan aiki ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, domin ba shi da wata kafa ta doka.

'Yan daban kungiyar G9 da ke adawa da gwamnatin kasar Haiti.
'Yan daban kungiyar G9 da ke adawa da gwamnatin kasar Haiti. REUTERS - RALPH TEDY EROL

Mai shari'a Enock Chacha Mwita ya ce "Kwamitin tsaron kasar ba shi da hurumin tura jami'an 'yan sanda a wajen Kenya."

Ya kara da cewa "Irin wannan hukuncin ya sabawa kundin tsarin mulki da doka don haka bai dace da tsarin mulki ba, ba bisa ka'ida ba kuma mara inganci."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.