Isa ga babban shafi

MDD ta amince da tura jami'an tsaro zuwa Haiti don murkushe 'yan daba

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin tura rundunar soji ta kasa da kasa zuwa Haiti, domin taimaka wa gwamnatin kasar kawo karshen ta’addancin kungiyoyin ‘yan daba masu dauke da muggan makamai.

'Yan daban kungiyar G9 da ke adawa da gwamnatin kasar Haiti.
'Yan daban kungiyar G9 da ke adawa da gwamnatin kasar Haiti. REUTERS - RALPH TEDY EROL
Talla

Manbobi 13 na Kwamitin Tsaron ne suka kada kuri’ar amincewa da kudurin fara aikin rundunar tsaron hadin gwiwar da za ta zama a karkashin jagorancin Kenya.

China da Rasha sun kauracewa nuna goyon baya ga  tura jami’an tsaron zuwa Haiti ne, saboda fargabar da suka ce suna da ita a kan yiwuwar sake rincabewar matsalar rashin tsaron kasar a maimakon samun sauki.

Tun a shekarar bara, Fira Ministan Haiti Ariel Henry ya yake rokon da kai musu taimakon jami’an tsaron kasa da kasa, biyo bayan karuwar hare-haren da kungiyoyin ‘yan daba ke kai wa a sassan kasar.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, ya ce kimanin rabin al’ummar Haiti da yawansu ya kai mutane miliyan 5 da dubu 200 ne ke bukatar agajin gaggawa, yayin da hare-haren ‘yan dabar ya raba akalla mutane dubu 200 da muhallansu.

A shekarar bana kadai, rayukan mutane dubu 3 suka salwanta, yayin da aka sace wasu dubu 1 da 500 don karbar kudin fansa sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi a kasar ta Haiti.

A watan da ya gabata ne kuma, tsohon dan sandan da ya rikide zuwa ‘uban daba’ Jimmy “Barbecue” Cherizier, yayi shelar aniyarsa ta neman kifar da gwamnatin Fira Minista Ariel Henry, lamarin da ya  kara jefa fargaba a zukatan ‘yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.