Isa ga babban shafi

Rikicin 'yan daba a Haiti ya lakume rayukan mutane dubu 2 da 400- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu 2 da 400 ne suka mutu sakamakon rikicin da ya barke a Haiti tun daga watan Janairu zuwa yanzu, ciki har da daruruwan da gungu-gungu na ‘yan sa-kai suka yi wa kisan rubdugu  a yayin da ‘yan sandan Kenya suka isa kasar don taimaka wa jami’an tsaro. 

Jami'an 'yan sandan Haiti masu fada da 'yan daba a kasar.
Jami'an 'yan sandan Haiti masu fada da 'yan daba a kasar. AP - Odelyn Joseph
Talla

Wannan rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin gungun-gungu na ‘yan daba a Part Au Prince, babban birnin Haiti ya yi sanadin mutuwar mutane 30 a cikin wannan makon. 

Kakakin Hukumar Kare Hakin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniyar, Ravina Shamdasani, ta shaida wa manema labarai a birnin Geneva cewa,  a tsakanin 1 ga watan Janairu na wannan shekarar, akalla mutane dubu 2 da dari 239 ne aka kashe, kana wasu 902 suka samu rauni. 

Bugu da kari, Shamdasani ta ce mutane dari 951 ne aka sace tun daga lokacin da rikicin ya tashi zuwa yanzu. 

A yayin da lamarin ke kara harzuka al’ummar yakunan  da abin ya shafa, ta yi kashedin cewa, ana samun karuwar kisan rubdugu a wasu sassa, tare da habakar kungiyoyi na kare kai da ramuwar gayya. 

A cikin ‘yan kwanakin nan, tarzoma da ta tashi a yankin Carrefour-Feuilles da ke makwabtaka da babban birnin Haiti ya tilasta wa mutane akalla dubu 5 tserewa daga gidajensu. 

Kisan gilla da aka wa shugaba Jovenel Moise a shekarar 2021 ne ya ta’azzara rikicin, inda gungun-gungu na ‘yan daba suka karbe iko da mahimman yanki na babban birnin kasar ta Haiti. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.