Isa ga babban shafi

Sama da mutane 600 sun mutu a rikicin 'yan daba a Haiti

Sama da mutane 600 suka mutu a wani kazamin rikicin 'yan daba a watan jiya a babban birnin Haiti kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar.

Jami'an tsaro na sintiri a titunan babban birnin Haiti.
Jami'an tsaro na sintiri a titunan babban birnin Haiti. REUTERS - RALPH TEDY EROL
Talla

Ofishin Babban Kwaminshinan Hukumar Kare Hakkin Bil'adma ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, a cikin watan Afrilu kadai, sama da mutane 600 ne aka yi wa kisan gilla a jerin tashe-tashen hankulan da suka shafi yankuna da dama a babban birnin kasar mai fama da matsalar tattalin arziki. 

Wannan na zuwa ne bayan wani rikicin da ya lakume rayukan mutane akalla mutane 846 a cikin watannin ukun farko na wannan shekara ta 2023 a kasar, baya ga 393 da suka jikkata da kuma 395 da aka yi garkuwa da su a tsakankanin watannin.

Wannan ya nuna cewa, an samu karuwar kashi 28 na tashe-tashen hankula a kasar idan aka kwatanta da rubu'in da ya gabata.

Haiti wadda ita ce kasa mafi fama da talauci a yankin Amurka, ta gamu da tarin matsaloli na tattalin arziki da siyasa tun daga watan Yulin 2021, lokacin da aka yi wa shugaban kasar Jovenel Moise kisan gilla.

Yanzu haka 'yan daba ne ke rike da ikon wurare da dama a babban birnin Port-au-Prince na kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.