Isa ga babban shafi
Haiti

An kama tsohon dan majalisar Haiti a Jamaica kan kisan tsohon shugaban kasa

‘Yan sandan Jamaica sun cafke wani tsohon dan majalisar dokokin kasar Haiti da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa shugaban kasa.

'Yan sandan kasar Jamaica
'Yan sandan kasar Jamaica © Hans Deryk/Reuters
Talla

Wata majiyar ‘yan sandan Jamaica ta ce an kama tsohon Sanata John Joel Joseph a tsakanin Juma'a zuwa Asabar ne, bayan shafe tsawon lokaci ana nemansa ruwa a jallo tun ranar 7 ga Yuli na shekarar 2021, lokacin da aka kashe shugaban Haiti Jovenel Moise.

Majiyar ta ce 'yan sandan Jamaica sun yi aiki ne tare da takwarorinsu na kasa da kasa kafin cafke tsohon dan majalisar.

An kashe tsohon shugaba Moise ne tare da jikkata matarsa da munanan raunuka a lokacin da gungun makasa kusan 20 suka kutsa cikin gidan shugaban kasar na Haiti tare da bude musu wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.