Isa ga babban shafi
Amurka - Bakin-haure

Dubban 'yan ci rani daga kasashen Latin da Haiti sun tunkari Amurka

Dubban 'yan ci rani da suka fito daga Haiti, da yankunan Kudancin Amurka da kuma Amurka ta Tsakiya sun soma tattaki daga kudancin Mexico zuwa arewacin kasar a ranar Asabar, inda suka yi arangama da jami'an tsaro dake kokarin dakile balaguron nasu.

Ayarin 'yan ci rani dake kokarin isa kasar Amurka.
Ayarin 'yan ci rani dake kokarin isa kasar Amurka. © REUTERS/Jose Torres
Talla

Wasu daga cikin dubban Bakin Hauren dake kokarin ratsa arewacin Mexico sun bayyana fatan isa kan iyakar Amurka, inda adadin 'yanci ranin da ke kokarin shiga kasar ya ninka wanda aka saba gani a watannin baya.

Wata kididdiga ta nuna cewar kimanin bakin hauren dubu 3,000 da suka kunshi iyalai da yara kanana ne, suka fara tafiya da kafa a ranar Asabar daga garin Tapachula a kusa da kan iyakar Mexico da Guatemala.

Bayanai sun ce a wani wurin binciken ababen hawa dake garin na Tapachula jami’an tsaro kimanin 400 sun yi kokarin dakile ayarin dubban bakin hauren, sai dai da yawa daga cikin ‘yan ci rainin sun yi nasarar wucewa.

Daya daga cikin wadanda ke jagorantar ayarin 'yan ci ranin Irineo Mujica, ya ce yana jagorantar balaguron zuwa birnin Mexico ne daga nan kuma su karasa Amurka, don nuna bacin rai da rashin samun taimakon gwamnati a yankinsu na Latin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.