MDD ta fara shirin tura jami'an tsaro zuwa kasar Haiti
Yau Litinin ake sa ran Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a kan kudurin tura jami’an tsaro na kasa da kasa zuwa Haiti, inda za su shafe shekara guda suna taimaka wa kasar wajen kawo karshen gungun kungiyoyin 'yan daba masu dauke da muggan makamai da ke haddasa tashe-tashen hankula.
Wallafawa ranar:
Bayan yakar masu aikata miyagun laifukan, ana sa ran rundunar za ta taimaka wa mahukuntan Haiti wajen maido da cikakken tsaro a sassan kasar, domin gudanar da zaben da aka shafe tsawon lokaci ana jinkirta shi.
Tun a ranar Asabar da ta gabata, Amurka ta gabatar da kudurin tura rundunar jami’an tsaron ta kasa da kasa zuwa Haiti, wadda Kenya ta ce a shirye take ta jagoranta.
A karkashin kudirin da za a kada kuri’ar a kai dai, rundunar jami’an tsaron da za a tura Haiti ba ta cikin rundunonin Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasashe, zalika za a samar da kudaden gudunawarta ne daga gudunmawar da kasashe za su bayar a bisa radin kansu.
Dangane da wa’adin zaman dakarun a Haiti kuwa, kudurin ya fayyace cewar bayan watanni tara, za a iya sake nazari kan kara lokacin da jami’an tsaron na kasa da kasa za su dauka suna yaki da kungiyoyi masu makamai a kasar zuwa sama da shekara guda.
Wasu alkaluma da aka fitar sun nuna cewar, yawan jami’an ‘Yan Sandan Haiti ba su wuce dubu 10 ba, yayin da yawan al’ummar kasar ya zarta sama da mutane miliyan 11.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu