Algeria ta kaddamar da Masallaci mafi girma a Afrika
Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune, a hukumance ya bude babban Masallacin kasar, wanda shi ne Masallaci na uku a yanzu mafi girma a duniya kuma na daya a nahiyar Afirka.
Wallafawa ranar:
Katafaren masallacin da zai iya daukar masallata dubu 120 a lokaci guda, an fara gudanar da sallah a cikinsa ne a watan Oktoban 2020, a lokacin shugaban kasar ke fama da cutar Covid-19 da ta hanashi halarta.
Masallachin da ake kira da Great Mosque of Algiers, na da hasumiya mafi tsayi a duniya, inda ta kai mita 265 kwatan-kwacin kafa 869.
An kwashe sama da shekaru 7 ana aikin gina shi, kuma an yi amfani da kadada 27.75 wajen tsara ginin masallacin.
A cikin Masallacin, akwai filin saukar jirgi mai saukar ungulu da kuma katafaren dakin karatu da zai iya daukar litattafai har miliyan daya.
A yanzu Algeria ce kasa ta farko da ke dauke da katafaren Masallaci a wajen biranen Makka da Madina, kuma ana sanar al'ummar musulmi za su yi amfani da masallacin wajen gudanar da ibada a lokacin azumin watan Ramadan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu