Isa ga babban shafi

Kwararru sun samar da na'urar magance cutukan numfashi a Kenya

Kwararru kan fasaha da harkokin lafiya a Kenya, sun fara amfani da na’ura mai amfani da fasahar dan adam wajen magance cutar tarin fuka da sauran cututtuka masu yaduwa ta numfashi.

Bullar annobar Covid19 na daga cikin abin da ya sanya kasashe suka fara shirin ko ta kwana, musamman bangaren da ya shafi cutukan numfashi.
Bullar annobar Covid19 na daga cikin abin da ya sanya kasashe suka fara shirin ko ta kwana, musamman bangaren da ya shafi cutukan numfashi. © WHO
Talla

Jagoran tawagar kwararrun Dr Videlis Nduba ya ce an zabi  fara gwajin da cutar tarin fukar ne la’akari da yadda take kara yaduwa a tsakanin jama’ar kasar.

Ya ce ana amfani da na’urar wajen nadar sautin tarin dan adam, kuma nan take zata saurari tarin sannan ta sanar cewa na tarin fuka ne ko kuma kawai tari ne na yanayi.

Bayanai sun ce tuni aka fara amfani da nau’rar wajen magance cutar kan wasu mutane.

Sai dai har yanzu hukumar lafiya bata fitar da matsayar ta kan wannan sabon salo na ganowa da kuma magance cutar ba.

A nata bangaren hukumar lafiya ta duniya ta ce ba zata amince da wannan sabuwar fasaha ba, har sai ta tabbatar da cewa tana aiki kaso 90 cikin 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.