Isa ga babban shafi

Dakarun Afrika ta kudu biyu sun mutu a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Wasu sojojin Afirka ta Kudu biyu sun mutu a kan aikinsu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, kamar yadda rundunar sojin kasar ta sanar a yau Asabar, a wani harin da bindiga daga wani sojin kasar."Lamarin ya faru ne a lokacin da daya daga cikinsu ya harbe dayan har lahira da makamin da yake amfani da shi kafin ya juya makamin a kan kansa tare da yin kisa," in ji rundunar tsaron kasar Afirka ta Kudu a cikin wata sanarwa.

Dakarun wanzar da zaman lafiya ayankin Goma
Dakarun wanzar da zaman lafiya ayankin Goma AFP - ALEXIS HUGUET
Talla

Sanarwar ta rundunar Afrika ta kudu ta SANDF ta ce sojojin da suka mutu an jibge su ne a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a matsayin wani bangare na rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta MONUSCO, wadda ta fara janyewa daga gabashin kasar da yaki ya daidaita. Kimanin karin dakaru 2,900 na Afirka ta Kudu ne aka jibge a DRCongo a matsayin wani bangare na rundunar raya kasashen kudancin Afirka (SADC) da aka tura domin taimakawa gwamnati wajen yakar 'yan tawayen M23.

Yankin Goma na DRCongo
Yankin Goma na DRCongo AFP - ALEXIS HUGUET

An kashe biyu daga cikin wadannan sojojin a watan da ya gabata a wani hari da aka kai musu da manyan makami, lamarin da ya janyo korafe-korafe daga jam'iyyun adawa na Afirka ta Kudu cewa an tura su ba tare da isassun tallafin da kayan aiki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.