Isa ga babban shafi
TA'ADDANCI

Muna gargadin Rwanda akan Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo - Faransa

Faransa ta bukaci Rwanda da ta kawo karshen duk wani goyon bayan da take bai wa 'yan tawayen M23 a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Shugaban Jamhuriyar  Dimokradiyyar Congo, Felix Tshisekedi daga dama, tare da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a birnin Kinshasa, ranar 4 ga Maris, 2023.
Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Felix Tshisekedi daga dama, tare da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a birnin Kinshasa, ranar 4 ga Maris, 2023. © Samy Ntumba Shambuyi/AP
Talla

Gwamnatin Paris ta ce ta damu matuka da halin da ake ciki a Gabashin kasar, musamman a yankunan Goma da Sake.

Sanarwar ta kara da cewa harin da ake kai wa kan 'yan gudun hijirar Jamhuriyar Congo ba abu ne da za a amince da shi ba, kuma dole ne kungiyar M23 ta dakatar da hare-harenta cikin gaggawa da kuma janyewa daga yankunan da ta mamaye.

Sanarwar ta Faransa ta zo ne daidai lokacin da Amurka ke gargadi game da halin tsaron da ake ciki a Congo, a wani taro da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar, tana mai gargadin Rwanda cewa ya kamata ta janye hannunta daga sha’anin tsaron kasar.

Dole ne kasashen duniya su dauki matakin gaggawa don dakatar da fadan da ake yi a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyya Congo, da kuma kawar da tashe-tashen hankula tsakanin kasar da Rwanda," in ji Robert Wood, mataimakin jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya.

Hakan ya biyo bayan gargadin da ta yi a ranar Asabar din da ta gabata, lokacin da Amurka ta yi Allah wadai da karuwar tashe-tashen hankula da ake dangantawa da 'yan tawayen M23.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta kuma yi kira da a janye sojojin Rwanda tare da neman gwamnatin Kigali ta janye na'urorinta na makamai masu linzami daga kasar, wadanda ke barazana ga rayuwar fararen hula.

Rwanda ta yi watsi da wannan kira da kuma zargin da ake mata, na rura rikici ga makwabciyarta.

Hukumomin Congo dai na zargin kasar da ke tsakiyar Afirka da goyon bayan kungiyar M23.

Jakadan Congo a Majalisar Dinkin Duniya, Zenon Ngay Mukongo, ya roki kwamitin sulhun ya bukaci janyewar sojojin Rwanda daga kasarsa, sannan ta ajiye duk wani goyon baya da take bai wa ‘yan tawayen M23.

Gwamnatin Congo dai na zargin dakarun Rwanda da mamaye wani yanki na lardin Kivu ta Arewa da ke gabashin kasar, duk domin tayar da zzaune tsaye da kuma kwashe musu albarkacin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.