Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa 'yan tawayen Jamhuriyar Congo takunkumai

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kakaba takunkumai a kan jagororin kungiyoyin ‘yan tawaye 6 da ke fada a sassan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, a yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a arewa maso gabashin kasar mai fama da rikici.

Wasu mayakan kungiyar 'yan tawayen kungiyar M23.
Wasu mayakan kungiyar 'yan tawayen kungiyar M23. REUTERS - JAMES AKENA
Talla

Kwamitin ya antaya takunkuman hana sayen makamai da na tafiye-tafiye a kan manyan jami’an kungiyar ‘yan tawayen Allied Democratic Forces (ADF) biyu, da kuma wani jagora a cikin kungiyar ‘yan tsagera ta Twirwaneho, da kuma wani guda daga kungiyar ‘yan tawayen National Coalition of the People for the Sovereignty of Congo (CNPSC).

Bugu da kari, an kakaba wadannan takunkumai a kan kakakin kungiyar ‘yan tawayen M23 ta ‘yan kabilar Tutsi, da kuma wani jagora a kungiyar ‘yan tawayen Democratic Forces for the Liberation of Rwanda (FDLR) ta ‘yan kabilar Hutu, wanda ya tsere daga Rwanda bayan da da aka yi kisan kare dangin da ya yi sanadin mutuwar ‘yan kabilar Tutsi da masu tausaya musu dubu dari 8 a shekarar 1994.

A wata sanarwa, mataimakin wakilin Amurka na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Robert Wood ya bayyana farin cikinsa da matakin kwamitin takunkumai a kan jagororin kungiyoyin ‘yan tawaye 6 a Congo, inda ya ce wadannan mutane ne ke da alhakin dimbim ayyukan cin zarafi a kasar.

Wannan matakin da Kwamitin Tsaron ya dauka a ranar Talata na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ake a arewa maso gabashin Congo ya daidata kusan mutane miliyan 7 a cikin shekaru 30 da suka gabata, a yayin da sama da kungiyoyi masu dauke da makamai 120 ke cin karensu babu babaka a kokarinsu na samun iko da yankin mai arzikin ma’adinai da albarkatun kasa.

Rikicin yankin ya ta’azzara ne tun bayan da ‘yan tawayen M23 suka sake daukar makamai a shekarar 2021, bayan shuru da suka yi na kusan shekaru 10.

Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Amurka da Majalisar Dinkin Duniya duk sun zargi Rwanda da mara wa ‘yan tawayen M23 baya, zargin da Rwanda ta musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.