Isa ga babban shafi

RSF ta koka biyo bayan kisan dan jarida a Chadi tare da iyalansa.

Kungiyar masu fafutuka ta Reporters Without Borders (RSF) ta yi Allah wadai a jiya Juma'a biyo bayan "mummunan kisan gilla" da aka yi wa wani dan jarida dan kasar Chadi tare da iyalansa."An harbe dan jarida mai suna Idriss Yaya na gidan rediyon al'ummar Mongo, da matarsa ​​da karamin yaronsu," in ji kungiyar yan jaridu ta kasa da kasa.

Wasu daga cikin yan kasar Chadi da rikici ya raba da gidajensu
Wasu daga cikin yan kasar Chadi da rikici ya raba da gidajensu REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Dan jaridar mai suna Idriss Yaya, a cewar kungiyar, a baya an yi barazana da kai masa hari" musamman "saboda labarin da ya yi game da rikice-rikicen yanki" a cikin kasar ta Chadi.

Kungiyar RSF
Kungiyar RSF AFP - PHILIPPE LOPEZ

Kungiyar yan jaridu ta kasa da kasa wato RSF ta kara da cewa "an kashe dan jaridar ne bayan an ambaci sunansa" a shafukan sada zumunta "a matsayin tushen bayanai kan yadda 'yan kabilar Moubis ke saye makamai ba bisa ka'ida ba.

Dakarun kasar Chadi
Dakarun kasar Chadi HYACINTHE NDOLENODJI via REUTERS - HYACINTHE NDOLENODJI

An kama mutane tara da ake zargi da "sun shirya kisan kai" kuma 'yan sandan yankin suna yi musu tambayoyi domin su tantance duk wani alhakin da ya rataya a wuyansu a wannan kisan, sanarwa daga kungiyar ta Reporters sans Frontiere.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.