Isa ga babban shafi

Rikicin kabilanci ya sake hallaka wasu mutane 23 a kudancin Chadi

Gwamnatin Chadi ta tabbatar da mutuwar mutane 23 a wani sabon rikici da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a karshen makon jiya bayan makamancinsa a makon jiya da ya hallaka tarin fararen hula duk dai a yankin kudancin kasar.

Wata tarzoma a Chadi.
Wata tarzoma a Chadi. © HYACINTHE NDOLENODJI via REUTERS
Talla

Sanarwar da ma’aikatar sadarwar Chadi ta fitar a jiya Litinin ta ruwaito ministan sadarwar kasar Abdraman Koulamallah na cewa rikicin ya barke a yankin Moyen-Chari na kudancin kasar ne bayan kisan wani makiyayi dan kabilar Larabawa.

Sanarwar ta ce rikicin ya fantsama zuwa kauyukan Chadi 3 tsakanin ranakun 17 zuwa 21 ga watan jiya kwanaki kalilan bayan faruwar makamancinsa game da takaddamar mallakar fili duk dai tsakanin kabilun biyu da suka kunshi bangaren makiyaya da na manoma.

A cewar Abdraman Koulamallah, tun farko bangaren manoman ne suka farmaki yankin da wani gungun makiyaya suka yada zango don ci rani, sakamakon zarginsu da mamaye musu fili, harin da ya kai ga rasa ran mutum guda.

A cewar ministan yayin mayar martani ne bangarorin biyu suka rika kashe juna a rikicin da aka kwashe tsawon mako guda ana yi, wanda ya kai ga kisan mutane 23 ciki har da Larabawa daga bangaren makiyayan da kuma mutane 14 daga bangaren kabilar Sara-Kaba da suka kunshi mata 4 da kananan yara 2.

Sanarwar da ma’aikatar sadarwar ta Chadi ta fitar ta ce tuni hankula suka kwanta bayan isar jami’an tsaro yankin da suka kwantar da tarzomar tare da kame wadanda ke da hannu a assasa rikicin.

Makamancin wannan rikici tsakanin al’ummar Chadi ba sabon abu ne inda a lokuta da dama akan rasa dimbin rayuka da zarar bangarori biyu suka zare makamai, rikicin da ake ganin faruwar irinsa hatta a wasu yankuna na kasashen Sudan da Sudan ta Kudu da jamhuriyar Afrika ta tsakiya da kuma Kamaru baya ga Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.