Isa ga babban shafi

Saliyo ta kafa dokar ta baci don yakar matsalar shan miyagun kwayoyi

Shugaban Salio Julius Maada Bio ya yi shelar kafa dokar ta baci da zummar kawo karshen matsalar shan miyagun kwayoyi a kasar.

Shugaban Saliyo Julius Maada Bio
Shugaban Saliyo Julius Maada Bio © AFP - Kola Sulaimon
Talla

Wannan mataki ya biyo bayan yadda aka fara samun matasan da ke laɓaɓawa cikin maƙabartu suna tone kaburbura, inda suke yi daukar kasusuwan mamata tare da nika wa don hada muguwar kwayar da suke kira da Kush, domin maye gurbin miyagun kwayoyin da ba sa iya saye.

Bincike ya nuna cewa saukin farashin muguwar kwayar ta Kush ya bai wa tarin matasan da ke zaman kashe wano a Saliyo damar sayenta, yayin da kuma suke iya samun karinta daga makwafciyarsu Liberia.

Wani rahoton gwamnatin Saliyo ya nuna cewar mutane da dama ne a kasar suka rasa rayukansu,, yayin da wasu suka haukace a dalilin shan muggan kwayoyin da suka hada da Tramadol, da Tentanyl da kuma Wiwi a tsawon shekaru huɗu da suka gabata.

Sai dai har yanzu gwamnatin ba ta kai ga fitar da adadin wadanda wannan masifa ta shafa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.