Isa ga babban shafi

Fari a Zimbabwe na shafar noman masara

Hukumomin Zimbabwe sun sanar cewa lardin arewacin Mazowe ta dade ta na fama da matsanancin fari, wadda ke cigaba da yin barazana wajen samar da hatsi musamman masara. 

Gonar masara a Zimbabwe
Gonar masara a Zimbabwe Alexander Joe / AFP
Talla

Rashin samun wadataccen ruwan sama a lardin ya yi sanadiyar kashe kadada miliyan daya na masara, dalilin da ya sa tuni hukumomin ƙasar su ka bukaci daukar matakin shigar da masara daga wasu ƙasashen don cike gibin da ƙasar ta rasa. 

Zimbabwe dai ta shafe tsawon lokaci ta na shigar da hatsi daga Afrika ta kudu, kuma ta na sa ran samun ƙarin hatsin daga Brazil. 

A cewar shugaban kungiyar manoman hatsi a ƙasar Tafadzwa Musarara, daga yanzu zuwa karshen watan Yulin shekarar 2025 mai zuwa, za su bukaci shigar da akalla ton miliyan 1 da dubu 100 na masara, dan amfanin mutane da dabbobi. 

Sama da kaso 80 na yankunan Zimbabwe ke fama da matsalar karancin ruwan sama, dalilin da ya tilasta shugaban ƙasar ayyana dokar ta baci a farkon watan Afrilun nan, matakin da su ma ƙasashen Zambia da Malawi da ke makotaka da ita suka dauka. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.