Isa ga babban shafi

An fara bincike kan bayanan sirrin Amurka da suka fallasa

Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta sanar da soma bincike kan wasu bayanan sirrin kasar musu alaka da Ukraine da suka bazu a kafofin sada zumunta na intanet.

Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky
Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky AP - Andrew Harnik
Talla

Kakakin Ma’ikatar Shari’a ta Amurka ya ce yanzu haka suna tattaunawa da Hukumar Tsaron kasar dangane da wannan batu wanda tuni aka fara gudanar da bincike a kai.

Manyan bayannan sirrin Amurka da suka shafi rikicin yakin Rasha da Ukraine har ma da wasu sirri da suka shafi kawayen Amurka sun bayyana a shafukan Tuwita da Telegram da Discord da dai sauran shafukan sada zumunta da muhawara a cikin 'yan kwanakin nan, kuma har yanzu wasu sabbin takardu dake kunshe da bayanan sirrin na ci gaba da fitowa.

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata Ma'aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta ce tana nazari sosai kan lamarin" kuma tuni ta mika batun ga ma'aikatar shari'a a hukumance.

Bayanan sirrin CIA

Jami'an Amurka sun shaida wa jaridar Washington Post cewa akasarin bayanan da suka fito sun yi dai-dai da kunshin rahoton Hukumar Leken Asirin Amurka ta CIA da aka raba a manya-manyan matakai a fadar White House da Hukumar Tsaro ta Pentagon da kuma Ma'aikatar Harkokin wajen kasar, sai dai an sauya wasu bayanan.

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun bayyana fallasar bayanan sirrin tsaron cikin gidan Amurka a matsayin abin kunya da takaici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.