Isa ga babban shafi
Saudiyya

Al’ummar Musulmi na gudanar da Aikin Hajji a Saudiyya

Kimanin yawan mutane sama da miliyan biyu ne suka je aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya, inda yawancinsu daga kasashen larabawa ke gudanar da addu’ar ganin kawo karshen zanga-zangar da ake gudanarwa a kasashensu.A gobe Assabar ne za’a yi hawan Arfa a birnin Makka mahaifar Annabi Muhammad (SAW).Aikin hajjin bana na zuwa ne bayan gudanar da zanga-zangar adawa da kasashen larabawa, boren da ya yi sanadiyar kawo karshen mulkin Hosni Mubarak na Masar da Zine al Abidina Ben Ali na Tunisia da Muammar Gaddafi na Libya. Wadanda ke tallafawa mahajjata masu karamin karfi.Ana gudanar da aikin Hajji ne duk shekara a kasar Saudiyya ga wadanda suka samu halin zuwa domin cika daya daga cikin shika shikan musulunci tare da neman gafarar Ubangiji da samun yardarSa. 

Harabar Massalacin Makka kewaye da Ka'aba
Harabar Massalacin Makka kewaye da Ka'aba AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.