Isa ga babban shafi
Afghanistan-Amurka

Karzai ya bayyana matakan huldar Afganistan da Amurka

Shugaban Kasar Afghanistan, Hamid Karzai, ya bayyana matakan da suke bukata na ci gaba da barin Amurka ta girke sojinta a cikin kasar, wadanda suka hada da samar wa al’ummar kasar ‘Yancinsu.Yayin da yake bude taron shugabanin kabilun kasar, na Jirga, Shugaba Karzai yace suna bukatar ‘Yancin kansu, kuma a cikin wannan rana.Shugaban ya shaida wa mahalarta taron na kwanaki hudu cewar, suna bukatar dangantakarsu da Amurka ta kasance na kasa da kasa, maimakon na Uwargijiya da bawa, da kuma dai na kai harin dare cikin kasar.Karzai ya kuma bukaci Amurka, da ta dai na gina wasu kungiyoyi da ke adawa da Gwamnati, inda yac, amincewa da haka ne kawai zai sa su dauki matsayin barin dakarun Amurka a kasar.Shugaban ya gargadi kasashen da ke makwabtaka da kasar, irinsu China da Russia cewar babu wata daga cikinsu da za’a bari ta sanya baki kan al’amurran kasar.Ya karkare da cewar, Amurka na da karfi, Amurka na da kudi da kuma filaye fiye da nasu, amma kuma su zakuna ne. 

Shugaban Afganistan Hamid Karzai lokacin addu'ar mutuwar  Burhanuddin Rabbani
Shugaban Afganistan Hamid Karzai lokacin addu'ar mutuwar Burhanuddin Rabbani Reuters/Omar Sobhani
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.