Isa ga babban shafi
Syria

Syria ta Tsaurara Matakan Tsaro

Dakarun kasar Syria sun tsaurara matakan kare birnin Damascus a yau, yayin da kasashen Larabawa da kasashen Yammaci na Turai, ke tursasawa MDD data zartas da kudirin la'antar Shugaban na Syria Bashae al-Assad.

Reuters
Talla

Bayanai na cewa kazancewar fada cikin makon da ya gabata yafi tsanani fiye da kowace rana cikin watanni 10 da aka yi ana bata-kashi.

Fararen hula 13 da soja 6 suka gamu da ajalinsu a yau.

A jiya Lahadi kuwa mutane akalla 80 aka kashe a rikicin kasar ta Syria. Ministan Harkokin Wajen kasar Faransa Alain Juppe ya ce zasu bukaci MDD ta dauki mataki kan mahukuntan kasar. Juppe wanda ke kan hanayar zuwa MDD ya ce lokaci ya yi da Kwamitin Sulhu zai dauki mataki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.