Isa ga babban shafi
Syria

Taron kungiyar Larabawa ya bada damar baiwa ‘yan tawayen Siriya makamai

Babban Taron kungiyar kasashen Larabawa da aka gudanar ya baiwa kasashen damar baiwa ‘yan tawayen kasar Siriya makamai domin yakar gwamnaton shugaba Bashar al-Assad, dama dai an bayyana cewar kungiyar na shirin baiwa 'yan tawayen kujerar wakilcin kasar ta Siriya a kungiyar  

Tutar Syria a gaban 'yan tawaye
Tutar Syria a gaban 'yan tawaye Reuters
Talla

Sakamakon babban taron na kungiyar kasashen Larabawa da aka kammala da marecen ranar Talata, ya baiwa kasashen Larabawa damar taimakawa 'yantawayen kasar Siriya masu fada da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad da Makamai, domin kariyar kansu.

Amma babban taron yafi maida hankali ne ga batun magance matsalar ta kasar Syriya ne a siyasance a maimakon kara dagula al'amurra.

Kasar Siriya dai ta zargi mai karbar bakuncin taron wato kasar Qatar da kuma Saudi Arebiya da tura makamai ga 'yan tawayen kasar.

Shugabannin Larabawan dai sun tabbatar da wancan batu, na mika Kujerar wakilcin kasar Siriya ga bangaren 'yan tawaye har a gudanar da zabe domin kafa gwamnati.

Kasashen Iraqi da Algeriya duka sun nuna rashin amincewa da bada Kujerar ga 'yan tawaye, a yayinda kasar Lebanon ta nisanta kanta daga wannan matakin na mika Kujerar Siriya ga 'yan tawayen

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.