Isa ga babban shafi
EU-Syria

Kasashen Taurai na samun matsin lambar Faransa da Birtaniya akan taimakwa ‘Yan tawayen Syria

Kasashen Faransa da Birtaniya na cigaba da matsawa kasashen Nahiyar Turai da su himmatu wajen aikawa da ‘Yan tawayen Syria makamai domin su fafata da dakarun kasar. Kasar Jamus dai ta ja baya game da batun na aikawa da makamai kasar ta Syria a yayin da ake wani taron kasashen yankin na tsawon kwanaki biyu.  

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Kacper Pempel
Talla

“A daya bangaren sai an taimakawa mutane, har ila yau sai an yi taka tsantsan wajen ganin cewa kada makaman su fada hanun baragurbi.” Inji Ministan harkokin wajen kasar Jamus, Guido Westerwelle.

Wannan taro shine farkon farin tattaunawar da za ta bude hanyar samun matsaya akan takunkumin da za a kakabawa gwamnatin Assad da kuma dage takunkumin aikawa da makamai kasaR, inda ake sa ran za samu madafa a ran 31 ga watan Mayu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.