Isa ga babban shafi
Syria

Yan tawaye a Siriya sun sami Kujera a kungiyar kasashen Larabawa

'Yan tawayen kasar Siriya sun sami Kujera a Zauren kungiyar kasashen Larabawa, gabanin babban taron kungiyar da za'a gudanar ranar Talata a birnin Doha. Wani babban jigo a kungiyar ya gayawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar yanzu haka an gayyaci bangaren 'yan tawayen a zaman taron da kungiyar zata gudanar

Hoton wakilan kungiyar daular Larabawa
Hoton wakilan kungiyar daular Larabawa REUTERS/Stephanie McGehee
Talla

Wannan gayyatar da kungiyar ta yiwa bangaren 'yan tawayen na shirin maye gurbin wakilin gwamnatin shugaban bashar al-Assad da wakilin 'yan tawayen na kasar Siriya masu fada da gwamnati, a taron kungiyar mai mambobi ashirin da biyu.

Gwamnatin shugaba Bashar al-Assad dai ta maida martani da kakkausar murya kan wannan batu, harma tana zargin kungiyar kasashen Larabawan da karkata matsayinta zuwa ga 'yan tawaye tsageru.

Wata kafar Tallabijin ta ambato cewar Qatar ce tayi shan Ruwan gaba, ta kuma keta ka'idar kungiyar domin baiwa bangaren 'yan tawayen da suka bada hadain Kai ga yadda zasuyi raba dai dai da Dukiyar kasar da 'yan kazagin kasar Amurka.

Wannan labarin dai ya zo ne a dai dai lokacin da shugaban 'yan tawayen Ahmad Mu'az al-Khatib ya bada sanarwar ajiye mukamin sa, abinda ya dada dakushe mutuncin kungiyar 'yan tawayen ga Idon kasashen yammacin Duniya.

Hakama Khatib yace zai gabatarwa babban taron jawabin sa a madadin al'ummar kasar Siriya, a yayinda jagoran gwamanatin hadin guiwa ta kasar zuwa birnin Doha Nizar al-haraki ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar Khatib na shirin jagorantar Ayarin al'ummar kasar Siriya a babban taron da za'a gudanar a ran Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.