Isa ga babban shafi
Pakistan

Ana jefa kuri’ar zabe a Pakistan cikin matakan tsaro saboda Barazanar Taliban

Al’ummar kasar Pakistan suka fara jefa kuri’ar zabe mai dimbin tarihi wanda a karon farko wata gwamnatin Farar hula zata mika mulki ga gwamnatin Demokradiyya bayan shafe shekaru Sojoji na mulki a kasar.

Mazabar Peshawar, a zaben kasar Pakistan
Mazabar Peshawar, a zaben kasar Pakistan REUTERS/Fayaz Aziz
Talla

Mutanen Pakistan suna fatar kuri’ar da zasu jefa za ta kawo sauyi a kasar musamman bangaren ci gaban tattalin arziki da kawo karshen matsalar wutar lantarki da kuma cin hanci da rashawa.

Dubban mutanen Paskitan ne dai suka yi jerin gwano domin kada kuri’rarsu duk da barazanar kungiyar Taliban da ta lan’anci zaben a matsayin ya sabawa addinin Islama.

Rahotanni daga Pakistan sun ce mutane uku sun mutu a wani hari Bom da aka kai a Karachi, a dai dai lokacin da al’ummar kasar ke kada kuri’a

Wani jami’an kiwon lafiya a asibitin Karachi Semi Jamili, ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa sun karbi gawawwakin mutane uku sannan mutane 21 ne suka jikkata.

Wannan kuma na zuwa ne duk da dubban jami’an tsaro da aka girke a runfunan zabe bayan kungiyar Taliban ta yi gargadin kai hare haren kunar bakin wake.

Tun kafin a fara jefa kuri’a ne gwamnatin Pakistan ta rufe kan iyakokinta da Iran da Afghanistan domin dakile kwararar mayaka daga kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.