Isa ga babban shafi
Pakistan

Sabon shugaban kasar Pakistan Nawaz Sherif ya lashi Takobin sauya tafiyar kasar.

Wannan dai na zuwa ne bayan nasarar da Nawaz ya samu a zaben shugabancin kasar da aka gudanar da ya nuna cewar Nawaz ya samu nasara akan sauran abokan karawar sa, a zaben da masana suka bayyana cewar ya samu fitowar jama'a, kuma an kammala kowa na murna. 

Nawaz Sharif shugaban kasar Pakistan na yanzu.
Nawaz Sharif shugaban kasar Pakistan na yanzu. AFP PHOTO / ARIF ALI
Talla

Shugaban kasar Nawaz Sherif, ya lashi Takobin hana kasar Amurka cigaba da mamaye kasar ta Pakistan tare da kai karshen tashin hankalin da kasar take fama da shi.

Kasar India ta taya Shugaban kasar murnar samun nasarar zaben da aka yi masa a wata Takarda da Piraiministan kasar manmohan Singh ya rattabawa Hannu.

India ta bayyana zaben a matsayin kafa Tarihi mai muhimmanci da kuma fatar sabon shugaban kasar zai taimaka ga kara kyautata huldar Diplomasiyyar dake tsakanin su.

A jawabinsa na farko a kafaifan watsa Labarai na radio da Tallabijin abokin hamayyar sa Imran Khan ya taya Nawaz murnar samun nasara, ya kuma taya daukacin al’ummar kasar murnar fitowa Kwan su da kwarkwata domin zabe, abinda ya kira cigaban kasar ta fanning Diplomasiyya.

Tsohon Jarumin wasar Cricket wanda ke jawabi daga Gadon Assibiti inda yake kwance yana Jinyar karayar daya samu a kwanan baya, yace zaben ya samu fitowar jama’a kuma kowa na murna, yanzu a cewar sa, kowa na sane da cewar za’a samu sauyi a makomar kasar ta Pakistan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.