Isa ga babban shafi
Iraqi

Mutane sama da 500 suka mutu a Iraqi a watan Mayu

Alkalumman Jami’an tsaro da kiwon lafiya sun ce Kimanin Mutane 500 suka mutu a kasar Iraqi cikin watan Mayu, Inda ake fargabar Iraki na iya abkawa ga rikicin babbancin akida. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga mahukuntan Iraqi su yi kokarin daukar matakan tunkarar rikicin Siyasar kasar wanda ke kokarin nuna gazawar gwamnati a fannin tsaro bayan ficewar dakarun Amurka a kasar.

Mutane sun taru a wani wuri da aka kai hare haren kunar bakin wake a Iraqi
Mutane sun taru a wani wuri da aka kai hare haren kunar bakin wake a Iraqi Reuters
Talla

Alkalumma daga Jami’an tsaro da jami’an kiwon lafiya sun ce kimanin mutane 503 ne suka mutu inda kuma wasu mutane sama da 1000 suka jikkata a wannan watan na Mayu.

Yanzu haka kuma kusan mutane 1000 ne suka mutu tsakanin watan Mayu da Afrilu.
Harin da aka kai na baya bayan nan da aka kai wa mabiya Akidar shi’a a sassan yankunan Bagadaza ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 200.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangarorin Iraqi mabiya Shi’a da Sunni su zauna su sasanta kansu domin ci gaban kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.