Jordan za ta fara gina cibiyar nukiliya
Hukumar sanya ido kan ayyukan nukiliya ta kasar Jordan ta amince kasar ta soma gudanar da aikin bincike domin kafa cibiyar nukiliya ta farko a kasar wadda take daya daga cikin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da ba ta da arzikin man fetur.
Wallafawa ranar:
A cewar shugaban hukumar Majad Hawwari, matukar dai aka kammala wannan aiki, cibiyar za ta samarwa kasar da makamashin da zai kai Megewat biyar.
“Amincewa da gudanar da aikin ya zo ne shekaru biyu bayan an gudanar da bincike.”
Rahotanni na nuna cewa kasar Korea ta ce za ta gina wannan cibiya wacce ake sa ran kammalawa a shekarar 2016.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu